Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:21:49    
Wurare daban daban na kasar Sin sun shirya shagulgulan al'adu iri iri da yawa don murnar bikin yanayin bazara

cri

A lokacin bikin yanayin bazara, wato sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin, wurare daban daban na kasar Sin sun shirya shagulgulan al'adu iri iri da yawa, wadanda suka kara halin faranta rai ga jama'a a ranar bikin, wadannan shagulgula sun hada da wasannin fasaha da aka nuna a dakalin nuna wasanni da tarurukan haikali irin na gargajiyar kasar Sin da nune-nunen littattafai da zane-zane da dai sauransu. Wadannan aikace-aikace sun wadatar da zaman rayuwar jama'a a ranakun bikin da kuma samar wa jama'a faranta rai sosai.

A birnin Beijing da birnin Shanghai da birnin Kwangzhou da sauran birane na kasar Sin, lokacin bikin yanayin bazara lokaci ne mai muhimmanci na nuna wasannin fasaha, ana nuna wasan kide-kide irin na symphony, da wasan kwaikwayo tare da nuna wake-wake da kide-kide da dai sauransu iri iri da yawa. A birnin Shanghai da birnin Kwangzhou da sauran wurare, kungiyar wake-wake da kide-kide ta Mantovani na kasar Italiya ta soma nuna wasanninta a zagaye a kasashen Asiya. Daga ranar 19 ga wannan wata, kungiyar wasan Ballet ta kasar Rasha ita ma ta nuna wasannin ballet da ke da lakabi "tafkin Swan" ga 'yan kallon birnin Beijing, wasan Opera da sauran wasannin da jama'ar farar hula suke son kallo su ma sun zama abu mai haske ga shagulgulan al'adun da aka shirya a bikin.


1 2 3