Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-21 17:21:49    
Wurare daban daban na kasar Sin sun shirya shagulgulan al'adu iri iri da yawa don murnar bikin yanayin bazara

cri

Mataimakiyar shugabar hukumar al'adu ta birnin Beijing Malama Wang Zhu ta bayyana a lokacin da ta ganawa da manema labaru cewa, a shagulgulan murnar bikin yanayin bazara da aka shirya a shekarar da muke ciki, shahararrun wasanni na da yawa, kuma ire-irensu na da yawa, sa'anan kuma karo-karon da aka yi wasannin fasahohi na da yawan gaske, yawan wasannin kide-kide da wake-wake da raye-raye da wasannin kwaikwayo da wasannin kundumbala da dai sauransu da aka shirya ya kai sau 200 ko fiye. Ta bayyana cewa, lokacin bikin yanayin bazara shi ne lokacin da aka shirya wasannin fasaha mafi yawa a birnin Beijing, a shekarar da muke ciki, shagulgulan al'adun da aka shriya irinsu na da yawan gaske, dadin dadawa kuma , an nuna sabbin sinima da yawa tare da nuna wasannin fitilu masu kyaun gani sosai, sa'anan kuma, ana nunin littattafai da yawa.

Malama Wang Zhu ta kuma bayyana cewa, jama'ar birnin Beijing suna son karanta littattafai tare da saurarar laccar da aka ba da da kuma kai ziyara a gidajen al'adu da sauransu.


1 2 3