A shekarar bara, jihar Guangxi ta kasar Sin ta gabatar da sabon shirinta na hadin guiwar mashigin teku na Bac Bo a fannin tattalin arziki. Bisa shirin nan, ban da kasashen Vietnam da Thailand, za a mayar da kasashen Malasiya da Singapore da Indonesiya da Philippines da Brunei da suransu kasashe da za su zama kasashe da za a hada kansu cikin yankin tattalin arziki na Bac Bo.
Malam Chen Wu, mataimakin shugaban jihar Guangxi ta kasar Sin ya yi hira da wakilnmu cewa, "sabon shirin nan zai ba da taimako wajen habaka fannoni da ake hadin guiwa a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, da gaggauta raya yankin cinikayya cikin 'yanci a tsakaninsu, da kara inganta hadin guiwarsu, da samar da sabbin hanyoyi da ake bi wajen bunkasa harkokin tattalin arziki".
Bisa ci gaba da ake samu wajen raya yankin tattalin arziki na mashigin teku na Bac Bo, za a kara habaka harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN musamman ma a tsakanin jihar Guangxi ta kasar Sin da Pan kasashen mashigin teku na Bac Bo.(Halilu) 1 2 3
|