Yayin da wakilinmu yake neman labaru a tashar jiragen ruwa ta birnin Qinzhou, sai ya ga kwal da sauran ma'adinai da ake saukewa daga jiragen ruwa da yawa, wadanda kuma aka kawo su ne daga kasar Vietnam da sauran kasashe na kungiyar ASEAN. Malam Wang Delun, wani jami'in karamar hukuma ta birnin Qinzhou ya nuna wa wakilinmu ma'adinan nan cewa, "wadannan bakaken ma'adinai kamar tama da Manganese dukanninsu an shigo da su ne daga kasashen waje. Ko shakka babu, birninmu zai zama wani babban sansani da kasar Sin ke shigowa da ma'adinai daga kasshen waje. Don ta masana'antu, birnin Qinzhou wata kasuwa ce da ke saye da sayar da danyun kayayyaki, sabo da haka yanzu wasu masana'antun haka ma'adinan tagulla da masana'antun narke karfuna na kasar Sin suna ta zuba jari a birnin."
Malam Wang Delun ya kara da cewa, a sakamkon karuwar ma'adinai da ake bukuta a kasar Sin, yawan ma'adinai iri-iri da ake shigowa daga kasashen waje ta hanyar birnin Qinzhou ma yana ta karuwa. Yawan kayayyaki da ake shigowa da su ko fitarwa ta hanyar tashar jiragen ruwa ta Qinzhou ya riga ya wuce na kasafin da aka tsara. Sabo da haka yanzu ana nan ana aikin habaka tashar nan.
Birnin Fangcheng da ke bakin teku ya yi iyaka da kasar Vietnam, kuma yana daya daga cikin manyan birane da ake yin cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Vietnam. Malam Zeng Lizhao, shugaban hukumar kula da harkokin cinikayya ta bakin iyakar kasa ta birnin Fangcheng ya bayyana wa wakilinmu cewa, "abubuwa da muke shigowa da su daga kasar Vietnam sun kunshi ganyayen Ti da wake mai launin kore da albarkatun teku da sauransu. Sa'an nan kuma muna fitarwa da kayayyaki masu aiki da wutar lantarki da kayayyakin saka da kuma kayayyakin gine-gine masu yawa zuwa kasar Veitnam."
1 2 3
|