Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-16 10:42:37    
Ana himmantuwa wajen kyautata muhallin birnin Beijing domin marabtar taron wasannin Olympic

cri

Amma, duk da haka Mr, Shi Hanmin ya amince da kasancewar matsaloli da dama wajen kiyaye muhallin birnin Beijing. Ya ce, nan gaba gwamnatin birnin Beijing za ta kora muhimmanci kan aikin rage yawan gurbatacciyar iska da ake shaka, wato ke nan sassan da abun ya shafa na birnin za su dauki matakai masu amfani na kyautata tsarin samar da makamashi, da rage yawan kazamcewar iska da motoci suke fitarwa da kuma kwantar da kurar da takan tashi a filayen ayyukan gine-gine.

Game da ayyukan kyautata tsarin samar da makamashi dai, hukumomin da abun ya shafa na birnin Beijing za su sanya babban karfi wajen gyara kananan murhun kwal da yawansu ya kai dubu 11 wadanda akan yi amfani da su a wassu gajerun gidajen kwana na tubali a wuraren dake karkarar birnin Beijing. Daga baya, Mr. Shi Hanmin ya fadi, cewa a wannan shekara, za a kammala aikin gyara tukunyoyi fiye da dubu 16 masu nauyin Ton kasa da 20 dake samar da iskar ko ruwan zafi ta hanyar kone kwal. 'Idan an kammala wannan aiki', in ji shi, 'akasarin na'urori za su yi amfani da iskar gas da kuma wutar lantarki maimakon kwal'.

Ko kuma sane da cewa, yanzu a nan birnin Beijing, akwai motoci miliyan uku, wadanda suke gurbata muhallin birnin. A shekarar 2006, huumomin da abin ya shafa na birnin sun rairaye tsofaffin motocin Taxi dubu 15 da kuma motocin bus dubu 3. an kuma tabbatar da cewa, za a rairaye sauran tsofaffin motoci dubu 300 nan da shekaru biyu masu zuwa.

An kuma bayyana cewa, sassan da abun ya shafa na birnin Beijing za su yi iyakacin kokari wajen daidaita maganar tashin kurar da aka yi a wassu filayen gine-gine da yawansu ya kai dubu 5 zuwa dubu 6 domin shawo kan gurbacewar muhallin birnin.


1 2 3