Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-16 10:42:37    
Ana himmantuwa wajen kyautata muhallin birnin Beijing domin marabtar taron wasannin Olympic

cri

A gun wani taron watsa labaru da aka shirya a kwanakin baya ba da dadewa ba, wani jami'i mai kula da harkokin kiyaye muhalli na gwamnatin birnin Beijing ya furta, cewa an samu sakamako mai faranta ran mutane a 'yan shekarun baya wajen hana da kuma shawo kan gurbacewar muhallin birnin Beijing. Nan gaba ma, gwamnatin birnin za ta ci gaba da zuba makudan kudade domin yan wannan aiki da kyau, ta yadda za a tabbatar da manufar da kasar Sin ta gabatar kan gudanar da "taron wasannin Olympic na kore-shar".

Da yake ana ta habaka yunkurin raya birnin Beijing, shi ya sa har kullum bangarorin da abun ya shafa na kasar Sin sukan mai da hankali sosai kan maganar gurbacewar muhalli, Musamman ma bayan da gwamnatin birnin Beijing ta cimma burinta na shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, gwamnatin kasar Sin da ta birnin Beijing sun fi sanya karfi wajen yin ayyukan kiyaye muhalli na Beijing. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, tun daga shekarar 2001, yawan kudin da gwamnatin birnin Beijing ta kashe wajen kiyaye muhalli ya dara kudin kasar Sin watao Renminbi Yuan biliyan 90. shugaban hukumar kula da harkokin kiyaye muhalli ta birnin Beijing Mr, Shi Hanmin ya fadi, cewa ware makudan kudaden da aka rika yi da kuma shawo kan gurbatacciyar iska da ake yi da kyau sun kyautata muhallin birnin Beijing sosai. Sa'annan Mr. Shi Hanmin ya ce, a shekarar 2006, yawan gurbatacciya iska da ake kira "sulphur dioxide" a Turanci da aka fitar a fadin duk birnin Bijing ya ragu da kashi 7.9 cikin 100 idan an kwatanta shi da na shekarar 2005. ban da wannan kuma, yawan muhimman gurbatattun abubuwa da ke cikin ruwa ya ragu da kashi 502 cikin 100 bisa na shekarar 2005. Hakan ya kyautata ingancin iska kwarai da gaske a sararin samaniya na birnin Beijing.


1 2 3