Ko da yake ya zuwa karshen shekarar bara, matsakaicin fadin gidajen kwana da ko wane mutum na kasar Sin ya samu, ya kai muraba'in mita 26, amma duk da haka fadin gidajen kwana da jama'a suka samu ya sha banban sosai. Wasu masu hannu da shuni sun sami gidajen kwana masu fadi da kayatarwa, sa'an nan kuma mutane masu karami da matsakaicin karfi ba su iya sayan gidajen kwana ba, sabo da hauhawar farashinsu. Malam Zhu Zhongyi yana ganin cewa, "gidajen kwana masu fadi ko kankanta suna shafar albarkatun jama'a. Bai kamata masu hannu da shuni su sami gidaje masu fadi fiye da kima ba, haka kuma mutane masu fama da talauci su ma su sami gidajen kwanansu. Idan an sayi kanana da matsakaitan gidajen kwana, yawan kudi da ake biya don sayen gidajen kwana ma zai ragu, wannan ya amfana wa mutane masu karami da matsakaicin karfi su sayi gidajen kwanansu. "
Daga binciken da aka yi, an gano cewa, yanzu, yawancin mazaunan garuruwa da na birane suna bukatar sayan kanana da matsakaitan gidajen kwana. Rabinsu suna son sayen gidajen kwanansu masu fadin muraba'in misalin mita 90.
1 2 3
|