Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-09 16:15:01    
Kasar Sin tana sa kaimi ga gina kanana da matsakaitan gidajen kwana domin jama'a

cri

A sakamakon ci gaba da ake samu wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin da daga matsayin zaman rayuwar jama'arta, mazaunan garuruwa da na birane na kasar suna kara neman samun gidajen kwana masu kyau. Amma kasar Sin kasa ce mai dimbin mutane da karancin filaye, da yake filaye da ake amfani da su wajen gina gidajen kwana ya yi ta habaka, kasar Sin tana kara fama da karancin filaye a cikin garuruwa da birane, haka kuma iyalan masu karami da matsakaicin karfi ba su sami isasshen kudi wajen sayan gidajen kwana ba. Da ganin haka a farkon shekarar bara, gwamnatin kasar Sin ta tsara sabbin manufofi game da harkokin gidajen kwana cewa, kanana da matsakaitan gidajen kwana wadanda fadin ko wanensu ba zai wuce murabba'in mita 90 ba za su zama muhimman gidajen kwana da za a gina a cikin garuruwa da birane. A karkashin jagorancin gwamnatin, yanzu ana yin gyare-gyare kan tsarin gidajen kwana na kasar Sin yadda ya kamata.

Malam Zhu Zhongyi, mataimakin shugaban kungiyar hadin guiwar kamfanonin masu gina gidaje ta kasar Sin ya bayyana cewa, "kasarmu ta gabatar da manufa game da mayar da kanana da matsakaitan gidajen kwana da su zama muhimman gidajen kwana a birane da garuruwa, dalilin da ya sa haka, shi ne domin na farko ba a iya samar da isassun kanana da matsakaitan gidajen kwana ga jama'a ba a yanzu, na biyu, an yi la'akari da karancin filaye a kasar Sin. Ban da wadannan kuma, mu yi koyi da wasu kasashe kamar Japan da Korea ta Kudu wadanda su ma suke fama da karancin filaye sosai, wadanda kuma suka kafa doka kan fadin gidajen kwana da ake ginawa. "


1 2 3