Mr. Li ya ce , mun tattara kudin Sin Yuan fiye da biliyan 2 don kyautata manyan ayyukan ba da wutar lantarki , kuma a kafin ran 30 ga watan Yuli na wannan shekara mun gama ayyukan . A
yanayin zafi, wadannan ayyukan sun ba da taimako kwarai da gaske .
Ban da Lardin Heilongjiang , hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin da sauran wurare su ma sun yi aikin share fage sosai don warware matsalar da za a fuskanta lokacin yin amfani da wutar lantarki mai yawa a yanayin zafi . A watanni 6 na farko na wannan shekara , Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya gina manyan hanyoyin ba da wutar lantarki na kilomita fiye da dubu 5 . Ta haka an kara karfin samar da wutar lantarki . Jama'a masu sauraro , yanzu sai ku 'dan shakata kadan, daga basani kuma za mu dawo domin ci gaba da kawo muku shirinmu na Me ka sani game da kasar Sin.(Ado) 1 2 3
|