Lardin Heilongjiang yana da wadatattun albarkatu . Fadin gonakai ya kai muraba'in kadada dubu 2800 , wato ya kai kashi 7 cikin 100 na duk fadin kasar Sin . A Lardin Heilongjiang ana iya bunkasa aikin noma da masana'antun man fetur da kuma masana'antun harhada magunguna .
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , Saboda tattalin arzikin kasar Sin ya sami bunkasuwa da saurin gaske kuma cikin dogon lokaci , shi ya sa a cikin 'yan shekarun da suka wuce , a nan kasar Sin aka fuskanci halin 'karancin wutar lantarki wanda ba a taba ganinsa ba a tarihi . A yanayin zafi na wannan shekara , galibin wuraren kasar Sin suna fuskantar halin karancin wutar lantarki . Saboda haka Wurare daban daban na Kasar Sin za su dauki matakai masu yawa don rage tsananin matsalar karancin wutar lantarki , kuma a kan manufar tabbatar da yawan wutar lantarkin da ke samarwa ga zaman yau da kullum na jama'a , za a biya bukatun sassa daban daban na zaman al'umma a wajen yin amfani da wutar lantarki .
A watanni 3 na farko na wannan shekara , yawan tashoshin ba da wutar lantarki na larduna wadanda suka dauki matakan kayyade yawan amfanin wutar lantarki ya kai 26 . Lardin Heilongjiang yana daya dake cikinsu . Daga karshen watan Yuni , wurare Masu yawa na kasar Sin sun fuskanci yanayi mai zafi sosai, abin da ya yi sanadiyyar 'karuwar amfani da wutar lantarki . Alal misali a Lardin Heilongjiang , yawan wutar lantarkin da aka yi amfani a wajen bude iyakwandishin ya kai kimanin kashi 40 cikin 100 na jimlar wutar lantarkin , saboda haka an kara sabanin samar da wutar lantarki . Kamfanin ba da lantarki na kasar Sin ya kimanta cewa , a yanayin zafi na wannan shekara a duk kasar za a fuskanci karancin lantarki na kilowatt miliyan 25. Don rage halin karancin wutar lantarki da tabbatar da aikin samar da wutar lantarki , wurare daban daban na kasar Sin sun dauki matakai masu yawa . Lardin Heilongjiang yana daya daga cikinsu.
Li Zongguo , kakakin watsa labaru na Kamfanin ba da wutar lantarki na Lardin Heilongjiang ya bayyana cewa , tun daga watan Satumba na shekarar bara , kamfaninsa ya fara aikin share fagen samar da wutar lantarki a wannan shekara .
1 2 3
|