Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 16:52:55    
Wani kwararren kiyaye babbar ganuwar kasar Sin mai suna Dong Yaohui

cri

A ranar 4 ga watan Mayu na shekarar 1984, Mr Dong Yaohui ya soma tafiye-tafiyensa a kan babbar ganuwa tare da abokansa guda biyu, sun sha wahaloli da yawa, amma Mr Dong ya bayyana cewa, a hakika dai, da na soma tafiye-tafiye a kan babbar ganuwa, babbar matsala gare ni ita ce rabuwa da muka yi da rukunin mutane da zaman rayuwarsu tare da rabuwar danginmu da abokanmu, a kowace rana, muna tafiya a tsakanin manyan tsaunuka, kai, na ji kamar yadda ni kadai nake zama a duniya, babu aminai da abokai, babu sauran mutane, irin wannan halin da nake ciki ya sa ni bacin rai sosai da sosai, amma bayan kwanaki 508 da muka yi tafiyar, sai muka ketare gundumomi da birane da yawansu ya kai dari, mun kammala shirinmu, sai kafofin watsa labaru suka bayar da labaransu, sai suka soma yin suna a duniya.

A shekarar 1985, Mr Dong Yaohui ya shiga karatu a jami'ar Beijing ta kasar Sin, a wannan lokaci, ya hada da wasu masana da kwararru, kuma shi kansa ya shiga kungiyar yin nazari kan babbar ganuwa ta kasar Sin, ya kara bude idonsa, a sa'I daya kuma ya shirya bayanan da ya rubuta dangane da abubuwan da ya ji ya gani a lokacin da yake yin tafiye-tafiye a kan babbar ganuwa, littattafan da ya rubuta dangane da babbar ganuwa sun sami karbuwa sosai daga wajen masu karantu, kuma sun ba da tasiri mai yakini a gida da waje. Mr Dong ya bayyana cewa, yanzu, ana kare da kuma gyara kashi daya cikin kashi uku na yankunan babbar ganuwa , sauran kashi daya cikin kashi uku suna lalacewa, sauran kashi daya cikin kashi uku kuma sun salwance. Bai kamata ba a bata lokacin kare ta. Ba ma kawai babbar ganuwa ta kasar Sin ce ba, hatta ma ita ta duk 'yan adam ne , kuma alamar wayewar kai ce ta duk 'Yan adam, dole ne a kiyaye ta sosai.(Halima)


1 2 3