Babbar ganuwar kasar Sin tana daya daga cikin manyan kayayyakin mamaki da 'yan adam suka kago. A karni na biyu, Kafin dinkuwar kasar Sin da sarkin farko na kasar Sin Qin Shihuang ya yi, sarakunan kasashe daban daban sun gina wasu kananan katangun tsaron kai , sa'anan kuma an hada da su don su zama babbar ganuwa. Bayan shekaru fiye da dubu, dauloli daban daban na kasar Sin dukansu sun kara tsawon babbar ganuwar da kuma kara gyare-gyare a kansu ta yadda aka kara tsawaita tsawon babbar ganuwar har zuwa hamadar da ke yammacin kasar Sin daga bakin teku da ke gabashinta, yawan tsawon babbar ganuwar ya kai dubban kilomita. Daga cikinsu, yankunan babbar ganuwar da daular Ming ta gina yau da shekaru 600 da suka wuce ya fi tsawo, kuma an kare su da kyau sosai. Kodayake Mr Dong Yaohui ya yi zama a wurin da ke dab da babban ginin tarihi wato shaharariyar ganuwar, amma bai yi tsammanin cewar wai ya zama wani kwararen kare babbar ganuwa ba.
Mr Dong Yaohui shi ne wani ma'aikacin hukuma ne da ke kula da karfin lantarki ta birnin Qinghuangdao a gabashin babbar ganuwar kasar Sin, yana son hawa kan duwatsu da tsaunuka, saboda haka ya kan yin cudanya da babbar ganuwar, donhaka yana son kara fahimtar abubuwa dangane da babbar ganuwar. ya bayyana cewa, tun daga lokacin da nake karami, sai na ga abubuwa da yawa dangane da babbar ganuwa, amma ban fahimce su sosai ba. Ni wani ma'aikaci ne kawai, amma ina son karanta littattafai da yawa dangane da babbar ganuwar, amma ban same su ba, sabo da haka na tsai da kudurin yin tafiye-tafiye a kan babbar ganuwar don gano abubuwa dangane da ita a idona na kaina.
1 2 3
|