Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-06 18:25:29    
Sin tana kokarin daukar matakai don sassauta mugun tasirin da sauye-sauyen yanayi ke kawowa

cri

Amma duk da haka, Sin tana ci gaba da fuskantar kalubale mai tsanani a fannin sassauta dumamar yanayi. Bisa nazarin da aka yi, an ce, nan da shekaru 50 zuwa 80 masu zuwa, yanayin kasar Sin zai karu da digiri biyu zuwa uku. Sabo da haka, Sin ta tsara manufofinta dangane da fuskantar sauye-sauyen yanayi cikin shirinta na samun bunkasuwa mai dorewa, ta kuma kafa hukumar musamman wadda za ta kula da tsara shirye-shiryen fuskantar sauye-sauyen yanayi. A sa'i daya, Sin za ta kuma yi kokarin aiwatar da hadin gwiwa tare da kasashen duniya a fuskar nazarin tasirin yanayi da kuma fuskantarsa.

A gun taron manema labaru da aka shirya a ranar 6 ga wata, shugaban hukumar kula da yanayin kasar Sin, Mr.Qin Dahe ya kuma bayyana wasu matakan da Sin za ta dauka a nan gaba wajen inganta nazarin tasirin yanayi da kuma fuskantarsa. Ya ce,"Sin za ta inganta nazarin sauye-sauyen yanayi kamar yadda ya kamata, kuma za ta kara sa ido a kan yanayi. A halin yanzu, tashoshin sa ido kan yanayi na kasar Sin suna barbazuwa cikin rashin daidaici, wato an fi samunsu a gabashin kasar Sin, a yayin da ba a samunsu da yawa a yammacinta. Gwamnatin kasar Sin za ta kara yin kokari, don kara sa ido a kan yanayi, ta yadda za a kara samun bayanai dangane da fuskantar sauye-sauyen yanayi."(Lubabatu)


1 2 3