Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-06 18:25:29    
Sin tana kokarin daukar matakai don sassauta mugun tasirin da sauye-sauyen yanayi ke kawowa

cri

A bayane ne Mr.Qin ya ce, a 'yan kwanakin nan, kwata kwacin zafin rana na Beijing ya kai wani matakin koli a tarihi, kuma a shekarar da ta gabata, an samu wasu miyagun yanayi a bakin teku da ke kudu maso gabashin kasar Sin, ciki har da mahaukaciyar goguwa, dukan wadannan ba su iya rabuwa da dumamar yanayin duniya.

An ce, hayaki mai guba shi ne muhimmin abin da ke haifar da dumamar yanayi, sabo da haka, a cikin shekaru da dama da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai a fuskar rage yawan hayaki mai guba da ake fitarwa, don neman rage mummunar illa da sauye-sauyen yanayi ke kawo wa bunkasuwar zaman al'umma da tattalin arziki. Mr.Qin Dahe ya ce,"Yau da shekaru da dama da suka wuce, Sin tana kokarin bunkasa makamashin da ke iya sabuntawa, kuma tana kyautata tsarin makamashi, misali, Sin ta kara bunkasa makamashin ruwa da na nukiliya da kuma yin amfani da su, kuma tana nuna goyon baya ga karkara da sauran yankunan da suka dace da su bunkasa makamashin da aka samu daga tsirrai ko kuma daga karkashin kasa da makamashin rana da na iska, ta yadda za a kara yawan makamashi mai tsabta da ake amfani da su shekara da shekaru. Bayan haka, kasar Sin ta kuma dauki matakan kiyaye muhalli, ciki har da kare gandun dazuzzuka da mayar da filayen gonaki zuwa gandun daji da raya yankuna masu ciyayi da dai sauransu, har ma an kara samun fadin dazuzzuka a cikin 'yan shekarun baya."


1 2 3