
Yau a nan birnin Beijing, shugaban hukumar kula da yanayin kasar Sin, Mr.Qin Dahe ya bayyana cewa, yau da shekaru kusan dari da suka wuce, yanayin kasar Sin da na duniya baki daya yana samun wani babban sauyi na karuwar dumama. A halin yanzu, Sin tana kokarin daukar matakai, don sassauta mugun tasirin da sauye-sauyen yanayi ke kawowa, a sa'i daya kuma, tana inganta hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen duniya a fannin nazarin tasirin yanayi da kuma fuskantarsa.
A gun taron manema labaru da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a yau ranar 6 ga wata, shugaban hukumar kula da yanayin kasar Sin, Mr.Qin Dahe ya tsamo magana daga wani rahoton nazarin yanayin duniya da aka bayar kwanan baya, ya ce, yau da shekaru kusan dari da suka wuce, yanayin duniya da na kasar Sin yana samun babban sauyi na karuwar dumama.
1 2 3
|