Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 15:48:01    
Kasar Sin tana yin kokari wajen sa kaimi ga samun ilmi cikin daidaici

cri

Ban da wannan kuma game da matakan ba da ilmi wanda ba na tilas ba kamar jami'o'i da makarantun koyar da fasahar sana'o'i, tun shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin tana daukar matakai a jere domin bayyana kudurinta wajen gaggauta yunkurin samun ilmi cikin daidaici. Alal misali, kasar Sin ta riga ta kafa wani tsari domin ba da taimako ga dalibai masu fama da talauci wajen karatu. Kuma bisa tsarin, an bai wa wadannan dalibai sukolashif, ko ba su rancen kudin karatu, ko kuma soke kudaden karatunsu. Ban da wannan kuma hukumomin ilmi na kasar Sin sun bukaci jami'o'i daban daban na kasar Sin da su tsara wani tsarin musamman don dalibai masu fama da talauci, wato da farko suka shiga jami'o'i, daga baya kuma a ba su taimakon kudi bayan da aka tabbatar da halin da suke ciki wajen fama da talauci, ta yadda za a ba da tabbaci ga ko wane dalibi da su iya samun damar karatu yadda ya kamata. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun riga sun rarrraba kudin yuan fiye da biliyan 20 wajen ba da rancen kudin karatu, kuma dalibai masu fama da talauci da yawansu ya kai miliyan 2.4 sun samun irin wannan taimako. Zan He, wani dabilin jami'ar jama'ar kasar Sin yana daya daga cikinsu, kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"na zo daga wani karamin kauyen da ke da wuyar zuwa na jihar Hunan da ke tsakiyar kasar Sin. Game da wani gida wanda yawan kudin shiga da ya samu a ko wane wata ya kadan ne, zai yi matukar wuya wajen biyan kudin karatu na yuan kusan dubu biyar. Amma bayan da gwamnatin kasar ta ba da rancen kudin karatu, ba zan damu da irin wannan kudin karatu da yawa ba, na iya karatu cikin kwanciyar hankali."

Bisa labarin da wani jami'in ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ya bayar, an ce, ya zuwa shekara ta 2010, gwamnatin kasar Sin za ta zuba kudin musamman na yuan biliyan hudu domin taimaka wa 'yan makaranta miliyan hudu masu fama da talauci wajen samun ilmin fasahohin sana'o'i.(Kande Gao)


1 2 3