Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 15:48:01    
Kasar Sin tana yin kokari wajen sa kaimi ga samun ilmi cikin daidaici

cri

Sun Qiao Yun wata manomiya ce ta yankin kabilar Hui mai cin gashin kai na jihar Ningxia da ke arewa maso yammacin kasar Sin, yanzu danta yana karatu a wata makarantar sakandare da ke wurin. Madam Sun ta gaya wa wakilinmu cewa, sabo da talaucin da take fuskanta, ta taba yin tunanin cewa, danta ba zai iya ci gaba da zuwa makaranta ba. Kuma ta ce,

"A lokacin da, idan dana ya shiga makaranta don karatu, to zan biya kudin yuan 120 a ko wane zangon karatu. Amma muna fama da talauci, shi ya sa ba mu da kudin karatu. Daga baya kuma an gaya mini cewa, a nan gaba ba za a karbi kudin karatu ba. Ina farin ciki sosai."

Wannan sabuwar manufar da ta faranta ran Sun Qiaoyun da danta an fara aiwatar da ita daga lokacin bazara na shekarar da ta gabata, kuma muhimmin abin da aka tanada a cikinta shi ne, gwamnatin kasar Sin ta soke dukkan kudin karatun da ya kamata 'yan makaranta na kauyuka marasa ci gaba wajen tattalin arziki da ke yammacin kasar Sin su biya lokacin da suke matakin ba da ilmin tilas na shekaru tara. Manufar ta kawo alheri ga 'yan makarantan firamare da sakandare fiye da miliyan 50 na kauyukan kasar Sin. Game da gidajen da ke da wadata, kudin yuan 100 ko 200 a ko wane zangon karatu bai taka kara ya karya ba, amma game da gidaje masu fama da talauci, kudin wani babban nauyi ne da ke bisa wuyansu. Haka kuma a shekarar da muke ciki, za a aiwatar da manufar a dukkan kauyukan kasar Sin. Sabo da kasar Sin tana bin manufar ba da ilmin tilas na shekaru tara, shi ya sa aiwatar da wannan sabuwar manufa ta shaida cewa, dukkan 'yan makarantar firamare da sakandare na kauyukan kasar Sin ba za su biyan kudin karatu ba a nan gaba.


1 2 3