Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-29 14:22:04    
Margaret Chan, sabuwar babbar daraktar kungiyar WHO

cri

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO wadda aka kafa ta a watan Afril na shekara ta 1948 wata hukumar musamman ta MDD wajen kula da harkokin kiwon lafiya. Kuma muhimman ayyukanta su ne sa kaimi ga shawo kan cuttuttuka masu yaduwa da wadanda su kan barke a wani yanki, da samar da kiwon lafiyar jama'a da jiyya da kuma kyautata su, da shirya kwas din horaswa kan kiwon lafiya da dai sauransu. Hu Qingli, tsohon mataimakin babban darakan kungiyar ya bayyana cewa,

"kungiyar WHO tana fuskantar kalubale iri daban daban masu tsanani. Har zuwa yanzu ba a iya shawo kan cuttuttuka masu yaduwa da yawa, amma a waje daya kuma sabbin cuttuttuka masu yaduwa suna bullowa. Ban da wannan kuma yawan mutanen da suke kamuwa da cuttuttuka marasa yaduwa yana karuwa."

Bayan da Madam Chan ta hau kujerar babbar daraktar kungiyar WHO, ta bayyana manufofin aikin da za ta dauka a nan gaba a gun taron manema labarai da aka shirya, cewa kyautata halin kiwon lafiyar jama'ar Afirka da lafiyar mata da yara na duk duniya muhimmin aiki ne da za ta maida hankali a kai a cikin wa'adin aikinta. Kuma ta ce,

"Afirka nahiya ce da ta fi samun cuttuttuka a duk duniya, shi ya sa ko shakka babu zan mai da hankali sosai kan lafiyar 'yan Afirka da ta mata da yara."(Kande Gao)


1 2 3