Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-29 14:22:04    
Margaret Chan, sabuwar babbar daraktar kungiyar WHO

cri

Madam Margaret Chan wadda shekarunta sun kai 59 da haihuwa ta taba zuwa kasashen Canada da Singapore da kuma Birtaniya bi da bi don kara ilminta, daga baya kuma ta samu digiri na PHD a fannin ilmin likitanci. A shekara ta 1994, ta fara kama mukaminta na shugabar hukumar kiwon lafiya ta HongKong. A shekara ta 1997, Madam Chan ta gamu da muhimmiyar jarrabawa ta farko bayan da ta zama shugabar hukumar.

A watan Mayu na shekara ta 1997, an gano cutar murar tsuntsaye a wani filin kiwon kaji na shiyyar HongKong, wannan shi ne karo na farko da dabbobin gida suka kamu da cutar murar tsuntsaye a HongKong. Daga baya kuma bayan watanni da dama, cutar murar tsuntsaye ta samu yaduwa cikin sauri sosai, kaji masu dimbin yawa suka mutu. Amma abin ban mamaki shi ne, wannan cutar da ta kan kawo barazana ga rayuwar tsuntsayen gida ta canza salo, har kuma tana iya harbar dabbobin gida har ma dan Adam. A watan Agusta na shekara ta 1997, wani yaro na HongKong ya mutu sakamakon kamuwa da cutar murar tsuntsaye, kuma shi ne mutumin farko da ya kamu da cutar a duk duniya.

Fuskantar irin wannan sabutar cuta, Madam Chan ta dauki tsattsauran matakai nan da nan, wato ta ba da umurnin yanke kaji miliyan 1.6. Zhu Zonghan, shahararren kwararren aikin likitanci ne wanda ya taba yin aiki tare da Madam Chan ya nuna yabo sosai gare ta. Kuma ya ce,


1 2 3