Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-29 14:22:04    
Margaret Chan, sabuwar babbar daraktar kungiyar WHO

cri

"ita wata mace ce wadda take da saukin kai, amma lokacin da take aiki, ta kan yanke shawara ba wata-wata. A wancan lokaci, ta tsai da kudurin yanke kaje miliyan 1.6 na HongKong a cikin kwanaki uku, wato ke nan a yanke dukkan kaje masu rai na HongKong a kwanaki uku. Wannan kuduri ya taka rawa sosai ga zamantakewar al'ummar HongKong."

A shekara ta 2003, cutar SARS ta barke. Madam Chan ta sake jure wahalolin da ke gabanta. A ko wace rana, ta fito a gaban kafofin watsa labarai don amsa tambayoyi iri daban daban masu gaggawa. Fuskantar irin wannan mumunar annoba wadda ta kashe mutane da yawa, Madam Chan ta kasance cikin natsuwa sosai. Kuma ta bayyana cewa,

"mu da mazaunan HongKong mun bi wannan hanya tare. Ya kamata su san wahalolin da muke gamuwa da su, da kuma fahimtar kalubalen da ke gabanmu. A gaskiya, a kan yi mini matsin lamba sosai. Ni wata mutumiya ce da nake son fadi magana ta gaskiya, shi ya sa na gaya wa mazaunan HongKong abubuwan da na sani, kuma ban gaya musu wadanda ban sani ba."

Kwarewar aiki ta Madam Chan ta samu amincewa daga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO. A watan Agusta na shekara ta 2003, ta samu kujerar shugabar sashen kiyaye muhallin halittu na kungiyar WHO, daga baya kuma ta zama mai ba da taimako ga babbar daraktar kungiyar wadda take kula da harkokin cuttuttuka masu yaduwa.

A watan Mayu na shekara ta 2006, tsohon babban daraktan kungiyar WHO Lee Jong-Wook wanda ya zo daga kasar Korea ta Kudu ya mutu sakamakon cutar toshewar jijiyoyin kwakwalwa. Shi ya sa kungiyar ta tsai da kudurin zabar sabon babban daraktan kungiyar a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata. Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da Madam Chan wadda ta riga ta tafiyar da ayyukan kiwon lafiya kusan shekaru 30 da ta taba zama 'yar takarar hukumar. A karshe dai ta ci nasarar zaben, kuma ta samu kujerar babbar daraktar kungiyar WHO, wa'adin aikinta shi ne watan Yuni na shekara ta 2012.


1 2 3