Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-26 15:09:33    
Yin aikin noma ta hanyar zamani ya kyautata halin baya-baya da ake ciki a kauyukan kasar Sin

cri

Manomi mai suna Liu Hongwei wanda ke zama a kauyen ya bayyana wasu abubuwa a kan yadda kauyensa da ba a zo a gani ba ya zama wani kauye mai arziki sosai. Ya ce, "wani babban dalilin da yasa haka shi ne domin kauyensa yana bunkasa aikin noma ta hanyar zamani. A ko wace shekara, 'yan fasaha na gundumarmu su kan shirya kos domin mu manoma, su gaya mana iri-iri masu kyau na masara da wake da sauran amfanin gona da ya kamata mu yi nomansu a gonakinmu. Haka kuma hukumar kauyen ta kan kai mu zuwa sauran wurare don yin ziyarar bude ido, ta yadda za mu iya yin koyi da sakamako da sauran kauyuka suka samu wajen yin aikin noma."

Yanzu, ana aikin noma da injuna, don haka akwai rarar 'yan kwadago. Da ganin haka, an fara kafa masana'antun gyara amfanin gona a kauyuka wanda suka dauki manoma aiki. A sakamakon bunkawar aikin masana'antu, ana bunkasa harkokin tattalin arzikin kauyen daga fannoni daban daban.

Ban da wadannan kuma an dora muhimmanci sosai ga kiyaye muhallin kauyen nan. Da Malam Fu Huating, hakimin kauyen ya tabo magana a kan wannan, sai ya bayyana cewa,?idan wani kauye ya gina wasu sabbin gidaje, to, ba zai zama wani kauye iri na sabon salo ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, a kare muhalli. Ya kamata, a dasa ciyayi da bishiyoyi da furanni a kewayen gidajen kauye, a kare muhallinsa da kyau, to, kauye zai zama wani iri na sabon salo. Idan an so kyautata halin baya-baya da ake ciki a kauyuka daga duk fannoni, to, wajibi ne a kare muhallinsa da kyau".(Halilu)


1 2 3