Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-26 15:09:33    
Yin aikin noma ta hanyar zamani ya kyautata halin baya-baya da ake ciki a kauyukan kasar Sin

cri

Wani tsoho mai suna Zhang Weiliang wanda ke da shakaru 75 da haihuwa a bana, yana daya daga cikin wadanda suka yi kaura zuwa kauyen a karo na farko yau da shekaru 50 da suka wuce. Da ya tabo magana a kan halin da ake ciki a kauyen a da, sai ya bayyana cewa, "a lokacin zuwana a nan, kauyenmu sauruka ne, inda akwai wani allon katako wanda a jikinsa aka rubuta cewa "kauyen Xingshisi". A cikin irin wannan hali ne, muka yi amfani da ciyayi wajen gina wasu bukkoki da ba a zo a gani ba, don suka zama wurarenmu na kwana. Idan an yi iska a dare, to, ko shakka babu, kashegari idan muka tashi daga barci, fuskokinmu za su rufe da rairayi. "

Toshon nan ya kan ce, zaman rayuwarsa a yanzu ya yi tamkar mafarki da yake yi. Yanzu, kashi 80 cikin dari na iyalan kauyen "Xingshisi" da yawansu ya kai kimanin 200 suna zama cikin kayatattun gidaje iri na zamani. Yawan kudin shiga da manoman kauyen ke samu ya kan karu a ko wace shekara. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, jimlar kudin shiga da kauyen nan ya samu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1 a shekarar bara.


1 2 3