Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-26 15:09:33    
Yin aikin noma ta hanyar zamani ya kyautata halin baya-baya da ake ciki a kauyukan kasar Sin

cri

Tun daga shekarar bara, kasar Sin ta fara yin ayyukan raya kauyukanta iri na sabon salo. A shekarar da ta wuce, ta kashe makudan kudade don ba da taimako wajen kyautata aikin noma da ayyukan zaman rayuwar manoma, ta yadda za a sassauta gibi da ke tsakanin birane da kauyuka. Daga cikinsu, canja hanyar da ake bi wajen yin aikin noma da raya aikin noma iri na zamani manyan ayyuka ne da take yi wajen raya kauyuka iri na sabon salo. Yanzu za mu gwada muku wani misali a kan yadda wani kauye wanda ke baya-baya a da ya zama kauye iri na sabon salo ta hanyar bunkasa aikin noma iri na zamani.

Akwai wani kauye da ake kira "Xingshisi" cikin Sinanci a lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Yau da shekaru 50 da suka wuce, wadanda suka yi kaura zuwa kauyen nan daga sauran wurare su ne suka gina wannan karamin kauye. A wancan lokaci, kauyen sauruka ne, ba ya da gonaki ko kiris, balletanama gidajen kwana. Amma yanzu, kauyan ya zama wani sabon kauye mai arziki wanda ya shahara a ko ina cikin lardin nan.


1 2 3