Sa'anan kuma sarkin Kangxi ya tura sojojinsa zuwa Taiwan, bayan yakin da ya yi da sojojin da ke mamaye a Taiwan ne, ya kafa hukumar daular Qing a Taiwan, ta hakan, sarkin Kangxi ya yi nasarar kiyaye cikakken yankin kasar Sin.
A arewa maso gabashin kasar Sin, dayake sojoji masu kai hari a wurare masu nisa na kasar Rasha sun shiga cikin yankunan kasar Sin tare da tada fitina mai tsanani har cikin shekaru fiye da goma, jama'a farar hula suna zaman rayuwa cikin mawuyacin hali, sai Kangxi ya yi yaki da su cikin shekaru 4, sarkin Rasha ya ga tilashi ne ya yi shawarwari kuma ya daddale yarjejeniya mai jituwa da daular Qing.
Sarkin Kangxi ya hau kujerar mulki har cikin shekaru 61, ya yi kokarin karatu sosai, ya ba da gudumuwa sosai a kasar Sin , shi ya sa mutane su kan kiransa da cewa, babban sarkin Kangxi.(Halima) 1 2 3
|