Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-24 15:01:59    
Wani tsohon sarki na daular Qing ta kasar Sin mai suna Kangxi

cri

A tsakiyar karni na 17, a kasar Sin, wani yaro mai shekaru 8 ya hau kan kujerar sarki ta daular Qing, sunan yaron shi ne Kangxi . Kangxi yana kan kujerar sarki har cikin shekaru 61, ya yi kokarin yin gyare-gyare kan harkokin kasa, ya kuma kai naushi sosai kan barkewar kasa da aka yi da kuma yaki da harin waje da raya tattalin arziki, ya bude wani sabon zamanin zinariya ga kasar Sin a tarihin mulkin gargajiya. Wadanda suka zo daga bayansa sun nuna masa yabo cewa, babban sarkinmu Kangxi.

A shekarar 1661, sarki mai suna Shun Zhi da ke da shekaru 26 da haihuwa ya mutu, sai nan da nan dansa na uku mai suna Aixinjuelo Xuanye da ke da shekaru 8 kawai da haihuwa ya hau kujerar sarki , shi ne babban sarki mai suna Kangxi. Dayake yana karami sosai a lokacin da ya hau kujerar sarki, shi ya sa wani babban wazirinsa mai suna Aobai ya taimaka masa wajen gudanar da mulkin kasa. Aobai shi kansa ya kan kiransa da cewa jarumi ne na farko, ya kware sosai wajen wasan karate. Tun lokacin da ya soma ba da taimako ga sarki wajen gudanar da harkokin mulkin kasa, sai ya soma mulkin danniya tare da matukar keta, wato mai kama karya ke nan, ya kulla rukuni-rukuni a fadar sarki, ya yi mulki shi kansa, mabiyansa na da yawa a cikin fadar sarki ko a waje. Lokacin da Kangxi ya cika shekaru 14 da haihuwa, ya kamata shi kansa ya soma gudanar da harkokin mulkin kasa, amma Aobai ya ki mika masa ikon aiwatar da harkokin kasa . Wani wazirin sarki ya gabatar da cewa, ya kamata Aobai ya mika wa sarki mulki, amma Aobai ya tilasta wa sarki Kangxi don kashe wannan waziri, saboda haka, Kangxi ya cika da fushi sosai a cikin zuciyarsa, amma bai bayyana sosai ba, bisa sunan wasa ne, ya zabi wasu samari 'yan gadi a fadarsa , kullum suke wasan karate har cikin shekaru biyu da suka wuce, amma Aobai bai lura da wannan ba. Wata rana, Aobai shi kansa ya shiga cikin fadar sarki, ba zato ba tsammani samari 'yan gadi sun fito fili sun yi wa Aobai kewaye sosai, kuma sun kife shi da kuma daure shi. Nan da nan sarkin Kangxi ya kira taro, ya sanar da laifufukan da Aobai ya yi, kuma ya kashe 'yanuwansa da mabiyansa duka duka, ya dawo da mulkin kasa a cikin hannunsa.


1 2 3