Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-24 15:01:59    
Wani tsohon sarki na daular Qing ta kasar Sin mai suna Kangxi

cri

A farkon lokacin da Kangxi ya soma aiwatar da harkokin kasa, halin siyasa da ake ciki ya kara tsanani sosai. Karamar kabilar Man ce ta kafa daular Qing. Kafin daular Qing, mulkin da kananan kabilu suka kafa a tarihin kasar Sin sai daular Yuan kawai, amma daular Yuan ta kasance cikin shekaru 100 kawai a tarihin kasar Sin . A lokacin da Kangxi ya cika shekaru 16 da haihuwa, sai shi kansa ya soma kula da harkokin mulkin kasa. Lokacin nan lokaci ne da daular Qing ta kafa mulkinta cikin shekaru 25 kawai, ta gamu da rikici sosai a cikin gida tare da harin da aka kai mata daga waje, ta sha wahalhalu da yawa, amma sarkin Kangxi ya magance dukan wadannan matsaloli cikin nutsuwa sosai, ya tsara manufofin kasa da aiwatar da harkokin kasa yadda ya ga dama.

A wancan lokaci, da akwai wasu tsofaffin janar ?janar na daular Ming da suka ba da kai ga daular Qing, kuma daular Qing ta nada su don zama sarakunan da ke karkashin mulkinta don yin gadi a wasu manyan wuraren da ke iyakar kasa. Wadannan sarakuna suna da sojoji da yawa a hannunsu, sun yi barazana sosai ga daular Qing. Shi ya sa sarkin Kangxi ya yi niyyar watsi da su, bisa sanadiyar nan ne, wani da ya fito daga cikin wadannan sarakuna mai suna Wu Sangui ya yi tawaye, ya ci amanar daular Qing, saboda haka sarkin Kangxi ya tattara manyan sojoji ya hallaka shi da 'yan tawayensa duka duka, an yi yake-yake cikin shekaru 8, a karshe dai sarkin Kangxi ya kashe Wu Sangui mai wayo sosai.


1 2 3