
'A cikin dogon lokaci, za a ci gaba da bunkasa wannan makabarta a fannonin tonon kayayyakin tarihi da kuma raya wurin yawon shakatawa, nan gaba ya kamata a yi la'akari da kafa wani babban dakin nune-nunen kayayyakin tarihi, inda za a nuna kayayyakin tarihi na daular Han da aka tono a lardin Shaanxi. Ta haka makabartar Hanyang za ta zama muhimmin wurin nune-nunen al'adun daular Xihan na kasar Sin.'
Ziyarar makabartar Hanyang ta sanya mutane su ji suna yin yawo a tsakanin abubuwan tarihi da na gaskiya. Masu yawon shakatawa kuma suna iya kara fahimtarsu kan tarihin daular Han ta hanyar idanunsu kai tsaye. Bayan da ya ziyarci makabartar Hanyang, Duan Jin, wani malami, ya bayyana cewa,
'Ina tsammani makabartar Hanyang ta kiyaye kyawawan al'adun kasarmu, wasu abubuwa sun ba ni mamaki sosai. Kasarmu ta kai matsayin sama-sama wajen fasahar kera kayayyakin tukwane da gine-gine. Al'ummarmu na da kyawawan al'adu, kamata ya yi a yada su. Mun gayyaci mutanen kasashen waje da su kai ziyara a nan, inda za su fahimci tarihin al'adu na kasarmu mai tsawon misalin shekaru dubu 5.'(Tasallah) 1 2 3
|