
A cikin wannan yanayi mai ban mamaki, mutane na iya ganin kayayyakin tarihi da yawa a kusa da su kuma daga fannoni daban daban, ta haka sun iya fahimtar zaman rayuwar sarakunan daular Han mai launuka iri-iri, haka kuma, sun iya kara fahimtarsu kan hanyoyin fasaha na zamani da aka bi wajen binciken kayayyakin tarihi da sake kyautata su da kuma nuna su.
A cikin dakin nune-nunen, an samu mutum-mutumi maza da mata da yawa masu tsirara, wadanda ba safai a kan ga irinsu ba. Kafin aka binne su, an sanya tufafi da hannaye na katako da ke iya motsawa a kan wadannan mutum-mutumi masu launuka iri daban daban. Amma saboda sun yi shekara da shekaru suna karkashin kasa, shi ya sa bayan da aka tono su, tufafi da hannayen katakon sun rube sun balle. Bullowarsu ta ba mutane mamaki sosai, har ma a idanun masana da yawa, su alamu ne da ke nuna ci gaban fasahar sassaka mutum-mutumi ta kasar Sin, an mayar da su tamkar Venus na kasashen gabashin duniya.
Haka zakila kuma, an tono mutum-mutumin dabbobi da yawa da aka yi da tukwane, aka kuma binne a cikin makabartar Hanyang. Wani masani mai ilmin binciken kayayyakin tarihi mai suna Li Li na Jami'ar Beijing ya nuna cewa, su ne mutum-mutumin dabbobi mafiya yawa da aka tono a duk kasar Sin har zuwa yanzu, wadanda suka fi kyan gani. Tabbas ne makabarta ta Hanyang za ta zama cibiyar nazarin al'adun daular Xihan a nan gaba. Ya ce,
1 2 3
|