Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-23 14:52:13    
Dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na makabartar Hanyang

cri

Dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na makabartar Hanyang na cikin birnin Xi'an mai dogon tarihi da ke yammacin kasar Sin. Makabarta ta Hanyang wuri ne inda aka binne sarki Liu Qi da kuma matarsa tare, wanda ya kafa daular Xihan mai matukar bunkasa. An fara gina ta a shekara ta 153 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.. Masu binciken kayayyakin tarihi sun fara tonon kayayyakin tarihi a wannan makabarta mai matsayi mafi koli tun daga farkon shekaru 1990. Ta fi girma a duk kasar Sin har zuwa yanzu, in an kwatanta da sauran gine-ginen tarihi na makabarta masu sarauta.

Shugaban dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na makabarta ta Hanyang Wu Xiaocong ya yi karin haske cewa,

'Makabarta ta Hanyang na cikin wuraren tarihi na rukuni na 5 da kasar Sin ta fi dora muhimmanci kan kiyaye su. Makabarta ta sarakunan daular Xihan da ke kunshe da kabarin Hanyang ta nuna fifiko wajen neman zama wurin tarihi na al'adu na duniya saboda albarkatunta.'

Fadin makabartar Hanyang ya kai misalin murabba'in kilomita 20, akwai manyan ramuka fiye da 190 a cikin wannan makabarta, sa'an nan kuma an tono mutum-mutumi da yawa da aka yi da tukwane a cikin manyan ramuka 81 na matsayin koli da ke kewayen kabarin sarki sosai. A kwanan baya, an bude dakin nuna manyan ramuka na makabartar Hanyang, shi ne dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na farko da aka kafa duka a karkashin kasa bisa tunanin zamani na kiyaye da kuma nuna kayayyakin tarihi a duk duniya a yanzu. A gun taron shekara-shekara na kwamitin kiyaye wuraren gargajiya na duniya a karo na 15 da aka yi a shekara ta 2005, an mayar da shi tamkar aikin da ya zama abin koyi a fannin kiyaye da nuna kayayyakin tarihi a duniya. Ban da wannan kuma, a cikin wannan dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na karkashin kasa na zamani, a kusa sosai da kabarin sarki, a karo na farko ne kasar Sin ta raba kayayyakin tarihi da masu yawon shakatawa a cikin wurare 2 da ke da yanayi iri daban daban, ta rufe kayayyakin tarihi gaba daya, ta kuma yi amfani da injunan zamani.


1 2 3