Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-12 14:56:29    
Bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan sun sami sabuwar damar hadin guiwarsu a fannin aikin noma

cri

Bisa sakamakon da aka samu a gun wannan taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan da aka yi a wannan gami, za a kara samar da dama mai yawa ga 'yan kasuwa na Taiwan da ke zuba jari a babban yankin kasar Sin don bunkasa harkokinsu. Malam Chen Fushi, babban dirketan zartaswa na reshen arewa maso gabashin Asiya na kamfani mai suna "Dachen" na Taiwan ya bayyana cewa, "a cikin shekaru da yawa da suka wuce, Taiwan ta sami fasahohi masu yawa wajen yin aikin kiwon dabbobi a fannonin kiwonsu da kula da su da kuma yi musu rigakafin cututtuka da sauransu. Idan an yi amfani da wadannan fasahohi a babban yankin kasar, to, yawan mutuwar kaji da ake kiwo zai kara raguwa, kuma za a kara daukar matakai wajen yi wa dabbobi rigakafin cututtuwa. Yawan kudi da manoma ke kashewa wajen kiwon dabbobi zai ragu."

Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan wannan taron dandalin tattaunawa, babban yankin kasar Sin yana kokari sosai wajen daukar matakai don aiwatar da sakamako da aka samu a gun taron nan. Nan gaba kuma zai gayyaci bangaren aikin noma na Taiwan don ya aika da kungiyoyinsa zuwa babban yankin kasar, don inganta ma'amala da ake yi a tsakaninsu, ta yadda za a gaggauta yalwata ma'amala da hadin guiwa a tsakanin bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan a fannin aikin noma.(Halilu)


1 2 3