A gun wannan taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar bangarori biyu a fannin aikin noma, babban yankin kasar Sin ya gabatar da sabbin matakai da dama wajen inganta hadin guiwar bangarori biyu a fannin aikin noma, don kafa wuraren hadin guiwar bangarori biyu a fannin aikin noma bisa gwaji, da gandayen noma domin manoman Taiwan, da ingiza cinikin amfanin gona a tsakanin bangarori biyu cikin sauki, da inganta ma'amalar aikin noma da ake yi a tsakanin bangarori biyu a fannin kimiyya da fasaha.
Dangane da wadannan sabbin matakai, Malam Chen Wuxiong, kwararre daga lardin Taiwan wanda ya dade yana kula da hadin guiwar bangarorin biyu a fannin aikin noma ya bayyana cewa, ta hanyar daukar wadannan matakai, za a samar da kyawawan gurabe don yin hadin guiwar bangarorin biyu a fannin aikin noma. Ya ce, "wadannan matakai za su kara ba da tabbaci ga aminan Taiwan da su zuba jari a babban yankin kasar. Bisa irin wadannan kyawawan sharuda, bangarorin biyu za su kara taimakon junansu a fannin filaye da kudin jari da 'yan kwadago da fasaha da kulawa da sauransu, don haka a ganina, za a yi sabbin ayyuka cikin hadin guiwarsu daya bayan daya."
1 2 3
|