Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-12 14:56:29    
Bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan sun sami sabuwar damar hadin guiwarsu a fannin aikin noma

cri

Tun daga shekarun 1980, wasu mutane kalilan na bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan suka fara hadin kansu a fannin aikin noma, amma yanzu, yawan kudi da a kan samu daga wajen cinikin amfanin gona da ake yi a tsakanin bangarorin nan biyu ya riga ya wuce dalar Amurka miliyan 900 a ko wace shekara. Taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar bangarorin biyu a fannin aikin noma da aka shirya a kwanakin baya ba da dadewa ba a birnin Bo'ao na lardin Hainan, ma'amala ce mai girma da aka yi a tsakanin bangarorin biyu a fannin aikin noma, wadda ba a taba ganin irinta ba a da. A lokacin taron, babban yankin kasar Sin ya fitar da manufofi da matakai da yawa don inganta hadin guiwar bangarorin biyu a fannin aikin noma. Wannan sabuwar dama ce da aka samu wajen zurfafa hadin guiwarsu a fannin aikin noma.

Da Malam Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ya tabo magana a kan makomar hadin guiwar bangarorin biyu a fannin aikin noma, ya bayyana cewa, babban yankin kasar zai kara habaka hadin guiwarsu a fannoni daban daban. Ya ce, "ya kamata, a habaka hadin guiwarsu a fannoni daban daban, a yi babban hadin guiwarsu a fannonin aikin noma da na daji da kiwon dabbobi da kamun kifaye da sauransu. A yi kokari wajen shigar da manoma na sana'o'i daban daban cikin hadin guiwar, ta yadda za su ci gajiyarsu. Ya kamata, a habaka ayyukan noman shuke-shuke da kiwon dabbobi da na gyara amfanin gona da sauransu a manyan wurarensu, a bunkasa masana'atu masu muhimmanci, a kara samu riba daga wajen sana'o'i daban daban ta hanyar zamani. "


1 2 3