Mr. Bush ya bayyana cewa, hafsoshin rundunar sojan Amurka sun sha yin bincike kan sabon shirin muhimman tsare-tsare a Iraki, ta yadda za a samu tabbaci ga kaucewa kuskuren da aka yi a da.
Sabo da babban matsin da ake yi wa gwamnatin Amurka sabo da yamutsatsen halin da ake ciki a kasar Iraki, shi ya sa cikin jawabin da Mr. Bush ya yi a wannan rana kuma ya kara sa kaimi ga gwamnatin Iraki cewa, dole ne ta tabbatar da makasudin da Amurka ta tsayar wajen kwanciyar hankali da siyasa da tattalin arziki na kasar Iraki cikin kayyadadden lokaci. Ya ce, "Na riga na bayyana wa firayim minista Nouri al-Maliki da saurna shugabannin Iraki cewa, alkawarin da Amurka ta dauka yana da kayyadadden lokaci. Idan gwamnatin Iraki ba ta iya tabbatar da alkawarinta ba, za ta rasa goyon baya daga jama'ar Amurka da jama'ar Iraki." (Umaru) 1 2 3
|