Bisa sabon shirin da aka tsayar an ce, sojoji masu ba da guzuri na Amurka za su shiga cikin kasar Iraki kafin karshen wannan wata. Domin gudanar da wannan sabuwar manufa, a wata mai zuwa wato lokacin Mr. Bush zai ba da rahoto ga majalisar dokokin kasa dangane da bayayin kasafin shekarar kudi, zai roki a ware kasafin kudi na dala biliyan 5.6 domin gudanar da shirin aika da sojoji masu ba da gudummawa, kuma za a ware dola biliyan 1.2 domin nuna goyon baya ga farfado da kasar Iraki, wato jimlar kudi ta kai dola biliyan 6.8.
Cikin jawabin da Mr. Bush ya bayar, karo na farko ne ya yarda da cewa, Amurka ta yi kuskure cikin yakin Iraki, kuma ya bayyana cewa, shi kansa zai dauki nauyin abun da ya faru sabo da wannan. Ya ce, "Kokarin da muka yi a da domin kiyaye kwanciyar hankali na Iraki ya ci hasara, muhimmin dalilin da ya sa haka ya kasu kashi 2 wato su ne, na farko sabo da ba a samu isasshun sojojin Iraki da na Amuka domin kiyaye kwanciyar hankali na mutanen Iraki ba, na 2 kuma shi ne, lokacin da sojojinmu suke gudanar da ayyukansu, sun gumu da fitinu da yawa wajen siyasa da rukunonin addini. Matakan soja da muka dauka ma sun gamu da kayyadewa sosai."
1 2 3
|