Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-11 15:54:38    
Shugaba Bush na Amurka ya yi bayyani domin daidaita manufar gwamnatinsa a Iraki

cri

A ran 10 ga wata, shugaba Bush na Amurka ya yi jawabi ga duk kasar ta rediyo mai hoto, inda ya bayyana sabon shirin da aka tsayar kan kasar Iraki, muhimman abubuwan da ke cikin wannan shiri suna hade da kara tura sojoji zuwa Iraki da ba da taimako ga Iraki domin farfado da kasar, ya yi haka ne domin kwantar da hargitsin da ake yi a kasar Iraqi. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya rubuto mana daga Amurka wanda yake da lakabin haka, "Shugaba Bush na Amurka ya yi bayyani domin daidaita manufar gwamnatinsa a Iraki"

Mr. Bush ya shafe minti 20 yana yin wanann jawabi ta rediyo mai hoto a wannan rana, cikin jawabin da ya yi ya sanar da cewa, Amurka za ta kara aike da sojojinta fiye da dubu 20 zuwa Iraki domin taimaka wa sojojin Iraki wajen kiyaye kwanciyar hankali na kasar. Ya ce, "Na tsai da kuduri cewa, za a kara aike da sojoji fiye da dubu 20 zuwa Irak, muhimman mutane daga cikinsu su ne, birgadiya masu yin fada guda 5 wadanda za a tsugunar da su a birnin Baghdaza, za su shiga cikin rundunar soja ta Iraki, wato za su yi fada da sojojin Iraki kafada da kafada."


1 2 3