Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-10 17:22:33    
Me ya sa kasar Amurka ta sake daukar matakin soja a kasar Somali?

cri

Da farko, kasar Somali muhimmiyar kasa ce da ke kusurwar Afirka, kullum kasar Amurka tana son ta yi sarrafa wannan kasa. Musamman ma a shekarun baya, an gano dinbim man fetur a kasar Sudan. An kiyasta cewa, yawan man fetur da ke akwai a kasar Sudan ya zama na biyu a duniya. Kuma kasar Sudan tana fitar da man fetur zuwa kasashen waje ta hanyar mashigin teku na Aden, kasar Somali da ke kudancin mashigin teku na Aden tana kare wannan hanyar sufurin man fetur. Kasar Amurka tana kara sarrafa wannan yanki, wannan dai wani mataki ne mai muhimmanci da ta dauka don aiwatar da muhimman tsare-tsaer na samun makamashi a duk duniya lami lafiya. A shekarar 2002, kasar Amurka ta fara girke sojojinta a kasar Djibouti, makwabciyar kasar Somali.

Na biyu, a cikin shekara daya da ta wuce, karfi na bangarorin dabam daban na kasar Somali ya canja, tun daga watan Yuni na shekarar 2006, dakarun kawancen kotunan Islama suka yi ta mamaye birane. A cikin lokacin rabin shekara, ya mamaye yawancin biranen kasar Somali, a cikinsu akwai Mogadishu, babban birnin kasar. Tasowar kawancen kotunan Islama, da manufofinsa sun yi kamar na kungiyar "Taliban" ta kasar Afghanistan. Yanzu, ko da yake dakarun kawancen kotunan Islama ya fadi, amma yana da tushen jama'a sosai a kasar Somali. Tasowar dakarun kawancen kotunan Islama ta zama wani kalubale ga kasar Amurka wajen sarrafa da kasar Somali.


1 2 3