Ran 8 ga wata, sojojin kasar Amurka sun tura jiragen sama na soja sun kai farmaki ga dakarun da ke kudancin kasar Somali wanda ake zargin su cewa wai 'yan kungiyar "al-Qaida" ne, wannan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa, wasu kuma sun ji rauni, kuma yawancinsu 'yan adawa da gwamnatin kasar Somali ne. Ran 9 ga wata, wani jami'in gwamnatin wucin gadi na kasar Somali ya tabbata cewa, a wannan rana jiragen sama na soja na kasar Amurka sun kai farmaki ga 'yan kungiyar 'al-Qaida' da ke kudancin kasar. Kafin wannan kuma, majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta sanar da cewa, sojojin Amurka sun riga sun girke jiragen ruwa na soja a tekun Somali, don hana 'yan kungiyar "al-Qaida" ficewa daga kasar.
Tun bayan kasar Somali ta shiga yakin basasa a shekarar 1991, kasar Amurka ta tura sojojinta zuwa kasar Somali saboda wai kiyaye zaman lafiya. A shekarar 1993, sojoji 18 na kasar Amurka sun mutu a wani aikin soja da aka yi a Mogadishu, daga baya, sojojin Amurka sun janye daga kasar Somali, kuma Majalisar dinkin duniya ta sakatar da aikin kiyaye zaman lafiya, sakamakon haka, ana yi ta yin yakin basasa a kasar Somali har zuwa yanzu.
Amma, yau bayan shekaru fiye da goma, ko me ya sa kasar Amurka ta sake sa hannu cikin yakin basasa na kasar Somali, kuma har ta kai farmakin soja a jere?
1 2 3
|