Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-10 14:35:49    
Mutanen Sin sun yi maraba da sabuwar shekara ta hanyar motsa jiki

cri

Ban da wannan kuma, a duk kasar Sin, a kudu da arewa, mutane da yawa sun hau babban dutse don maraba da sabuwar shekara. A ran 1 ga wannan wata na shekara ta 2007, an yi harkar hawan babban dutse na jama'a a cikin lokaci guda a wurare 12 na duk kasar Sin, wadanda suka hada da babbar ganuwa ta Badaling ta Beijing, da hasumiyar talibijin ta Tianjin da wurin shakatawa na Baizhai na Guangzhou da filin fadar Potala da dai makamantansu, inda mutane fiye da dubu 50 suka shiga ciki.

A birnin kankara na Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang, wasannin motsa jiki da aka zaba don maraba da sabuwar shekara ya fi jawo sha'awar mutane. Ko da yake zafin yanayin wurin ya kai digiri 20 ko fiye a karkashin sifiri, amma sanyi mai tsanani bai rage sha'awar da mutane ke nuna ga motsa jiki ba. A ran 1 ga wata, wato rana ta wasan iyo a lokacin hunturu, masu sha'awar iyo a lokacin hunturu sama da 180 ba su yi fargaba da iska mai sanyi ba, su yi iyo a cikin kogin Songhuajiang. Sun yi gwagwarmaya da sanyi mai tsanani da jikunansu masu zafi, wannan ya ba mutane matukar mamaki. Madam Tong mai shekaru 70 da haihuwa ta ce,'Ina sha'awar iyo a lokacin hunturu, na dade ina iyo a lokacin hunturu. Na zo Harbin daga Beijing don shiga wannan harka a wannan karo. Ina ganin cewa, wasan iyo a lokacin hunturu zai amfana wajen lafiyar jiki sosai, musamman ma wajen zuciya da huhu, sa'an nan kuma, na iya daidaita kalubale daga muhalli. Yin iyo a lokacin hunturu don maraba da sabuwar shekara ya nuna cewa, zan yi zaman lafiya a shekara ta 2007.'

Game da dalilin da ya sa mutane da yawa suka yi maraba da sabuwar shekara ta hanyar motsa jiki, shehun malama Huang Yaling, mai nazarin ilmin wasannin motsa jiki na zaman al'umma na jami'ar ilmin wasannin motsa jiki ta Beijing, ta bayyana cewa, saboda bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, shi ya sa zaman rayuwar mutanen Sin ya yi ta samun kyautatuwa, sun kuma mai da hankulansu kan ingancin zaman rayuwarsu. Lafiyar wani mutum ba ya nuna cewa, jikinsa na da lafiya kawai ba. An fi dora muhimmanci kan kiwon lafiyar jiki da tunani. Motsa jiki yana iya kyautata lafiya da sassauta matsin lamba ta fuskar ayyuka, har ma mutane su kan sami sabbin abokai a lokacin motsa jiki, suna iya kyautata zaman rayuwar al'adunsu. Maraba da sabuwar shekara ta hanyar motsa jiki ya nuna cewa, mutane suna kara mai da hankulansu kan lafiyarsu. Ta ce,'Da can mutane su kan taru su ci abinci tare a lokacin salla, amma yanzu sun fi son motsa jiki, wannan ya nuna cewa, mutanenmu sun kyautata fahimtarsu kan lafiya da motsa jiki, wannan kuma ya nuna cewa, za a yi ayyukan wasannin motsa jiki na jama'a cikin himma da kwazo a shekara ta 2007.'(Tasallah)


1 2 3