Saboda saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, yanzu zaman rayuwa na yau da kullum na mutanen Sin ya sami kyautatuwa sannu a hankali, sun kara mai da hankulansu kan lafiyarsu. A lokacin hutu don murnar sabuwar shekara ta 2007, mutane da yawa na kasar Sin sun yi maraba da sabuwar shekara ta hanyar motsa jiki.
A nan Beijing, babban birnin kasar Sin, saboda an yi kankara mai taushi, shi ya sa mutane kadan ne suka motsa jiki a waje, amma manyan cibiyoyin motsa jiki da dakunan wasa cike suke da mutane. Darektan cibiyar motsa jiki ta Qingniao ta Beijing Chen Huayu ya yi karin haske cewa, mutane da yawa sun yi ta yin rajista kan lokacin motsa jiki da malamai masu horas da motsa jiki ta wayar tarho a mako daya kafin lokacin hutu, yawan 'yan birnin da suka motsa jiki a wannan cibiya a wannan lokacin hutu ya ninka a kalla sau 3 bisa na yau da kullum.
A cikin cibiyar motsa jiki ta Qingniao, dukan injunan motsa jiki sun yi aiki ba tara katsewa ba, mutane sun ji dadin motsa jiki ko da yake sun yi gumi kamar sharaf-sharaf, malam Wang, wanda ke gudu a kan wani inji, ya gaya wa wakilinmu cewa,'Na ji babbar matsin lamba saboda aikina a kwanan baya, motsa jiki ya iya sassauta matsin lamba ta fuskar aiki, ya samar da wani sabon karfi a gare ni. Ina tsammani cewa, motsa jiki a rana ta farko na sabuwar shekara ya shaida cewa, zan kara mai da hankali kan lafiyata a cikin sabuwar shekara. A ganina, motsa jiki wata hanya ce mai yakini, yana da muhimmanci sosai a cikin sabuwar shekara.'
1 2 3
|