Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-08 14:46:16    
Kasar Sin ta dukufa kan kyautata yanayin karatu na 'ya'yan 'yan kwadago manoma

cri

Sabo da haka, ana daukar matakan wajen warware batun a wurare daban daban na kasar Sin. Alal misali, gwamnatin unguwar Haidian ta birnin Beijing ta zuba kudi yuan miliyan 13 domin kara girman makarantun da gwamnatin kasar Sin ta kafa da kuma sayen kujeru da tebura, ta yadda za a iya tsugunar da daliban da ke cikin makarantun 'ya'yan 'yan kwadago manoma cikin makarantun da gwamnatin kasar Sin ta kafa. Ji Man wadda muka amtaba a baya tana daya daga cikinsu.

Haka kuma a cikin birnin Wuxi na jihar Jiangsu da ke gabashin kasar Sin, gwamnatin wurin ta amince da 'ya'yan 'yan kwadago manoma da sauran yaran da ke zaune a wurin da su yi rajista tare don neman shiga makarantu, kuma ba a nuna bambanci wajen karbar kudin karatun ba, ta yadda 'ya'yan 'yan kwadago manoma suke iya shiga makarantun da ke kusa da gidajensu. Zhang Yizhong, mataimakin shugaban hukumar ilmi ta birnin Wuxi ya bayyana cewa, 'ya'yan 'yan kwadago manoma da yaran da ke zaune a wurin suna da damar bai daya waje samun ilmi. Kuma ya ce,

"yaran da suka zo daga sauran wurare da na wurin suna iya yin karatu cikin daidaici, ta yadda za su iya samun ci gaba tare, ta haka 'ya'yan 'yan kwadago manoma suna iya sabawa da zaman birane cikin sauri."(Kande Gao)


1 2 3