Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-08 14:46:16    
Kasar Sin ta dukufa kan kyautata yanayin karatu na 'ya'yan 'yan kwadago manoma

cri

A 'yan shekarun nan da suka gabata, an kafa wasu makarantu a wasu biranen kasar Sin domin daukar 'ya'yan 'yan kwadago manoma. Wasu daga cikinsu gwamnatin kasar Sin ta kafa su, wasu kuwa masu zaman kansu ne suka kafa. Lokacin da aka samar da dama ga 'ya'yan 'yan kwadago manoma wajen samun ilmi, wasu makarantu sun gaza wajen ba da ilmi kamar yadda ya kamata sakamakon rashin kudi da rashin malamai masu kwarewar aiki. Domin samar da yanayi mafi kyau wajen karatu ga 'ya'yan 'yan kwadago manoma, ana dudduba irin wadannan makarantu a wurare daban daban na kasar Sin, kuma ana cikin shirin rufe wusu daga cikinsu da ba su iya biyan bukatun da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ba wajen yanayin karatu. Yayin da kakakin ma'aikatar ilmi ta kasar Sin Wang Xuming ke zantawa wakilinmu, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki matakai domin bunkasa makarantu masu nagarta yayin da kuma rufe marasa nagarta. Kuma ya ce,

"Za a rufe makarantun da ba su iya biyan bukatun da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ba wajen yanayin karatu, da kuma wadanda ba a kafa su bisa abubuwan da aka tanada a cikin ka'idojin kasar Sin ba, sa'an nan kuma za a sake tsugunar da daliban da ke karatun a cikin wadannan makarantu yadda ya kamata, ban da wannan kuma za a nuna yabo da kuma goyon baya ga makarantu masu nagarta."


1 2 3