Kuma Mr. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta shigad da makarantun da aka kafa don 'ya'yan 'yan kwadago manoma cikin tsarinta na gudanar da makarantu bai daya, kuma za ta nuna goyon baya da kuma ba da jagoranci ga makarantun da ke dacewa da yanayin karatu a fannin filaye da kudaden kafa makarantu da kuma samar da horaswa ga malamai.
Game da makarantun da za a rufe kuwa, hukumomin kula da ilmi na wurare daban daban na kasar Sin sun bayyana cewa, za su tura daliban da suke cikin wadannan makarantu zuwa sauran makarantun firamare da sakandare da aka saba amfani da su. Ban da wannan kuma sun yi bayani a bayyane cewa, 'ya'yan 'yan kwadago manoma da sauran dalibai suna da hakkin bai daya wajen karatu, kuma makarantun da aka saba amfani da su ba su iya karya ka'idojin kasar Sin wajen kara karbar kudin karatu ba.
Ji Man, wata yarinya ce mai shekaru 12 da haihuwa da ta zo daga jihar Henan da ke tsakiyar kasar Sin. Yau da shekaru biyu da suka gabata, ta zo birnin Beijing tare da iyayenta, daga baya kuma ta shiga wata makarantar firamare wadda wani mai zaman kansa ya kafa. A watan Satumba na shekarar da muka ciki, an sanya ta a wata makarantar firamare da aka saba amfani da ita. Ta gaya wa wakilinmu cewa, yayanin karatu na wannan sabuwar makaranta ya fi kyau. Kuma ta ce,
" Ba a samu filin wasa a cikin makarantar firamare da na taba yi ba, shi ya sa idan lokacin motsa jiki ya yi, mu kan zauna cikin ajinmu don karatu, bugu da kari kuma malami guda ya kan koyar mana darrusa iri daban daban. Amma filin wasa na wannan sabuwar makaranta yana da girma, na iya motsa jiki, sabo da haka na ji farin ciki kwarai da gaske."
An taba yin gardama sosai kan matakan da kasar Sin ta dauka wajen rufe makarantun 'ya'yan 'yan kwadago manoma wadanda ba su da inganci. Wasu manoman da suka shiga birane don neman samun aikin yi sun yi shakkar cewa, makarantun da gwamnatin kasar Sin ta kafa za su nuna bambani ga 'ya'yansu. Wasu kuwa sun nuna damuwa kan cewa, yawan kudin karatun da makarantun da gwamnatin kasar ta sanya ya yi yawa.
1 2 3
|