Ban da wannan kuma dalilin da ya sa aka tada hargitsin Somali ya shafi kasashe da yawa. Sabo da kasar Habasha kasar ma'abuciya ce ta Amurka, shi ya sa wannan hargitsi ya bayyana kiyayyar da ake yi tsakanin kungiyoyi Habasha masu nuna goyon baya ga Amurka da dakaru Larabawa. Abun musamman shi ne Amurka ta la'anci dakarun rukunonin addinai na Somali da su gama gwiwa da kungiyar "Al-Qaida" a asirce, amma shugabannin rukunonin addanai na Somali kuma sun yi kira ga musulmi masu hidima na sa kai na duk duniya da su je kasar Somali don yin yakin jahadi na kasar Habasha, wannan ya kara rikita hargitsin Somali sosai.
Sabo da abubuwa da yawa da aka ambata baya, shi ya sa shawarwarin gaggawa da Katar, shugabar kwamitin sulhu na wannan zagaye take bukatar yin shawarwarin a ran 26 ga wannan wata shi ma bai samu sakamako mai yakini ba. Kasar Katar ita ce kasar Larabawa daya tak dake cikin kwamitin sulhu, sanarwar shugaba da ta rubuta ta jaddada magana cewa, ya kamata Habasha ta janye sojojinta daga kasar Somali, amma ta gamu da rashin amincewa daga wajen Amurka da Ingila da sauran kasashe. Wadannan kasashe sun bayyana cewa, sojojin Habasha sun je kasa Somali ne bisa gayyatar da gwamnatin wucin gadi na Somali ta yi masu domin ba da taimako ga kasar.(Umaru) 1 2 3
|