Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-28 16:15:44    
Wace Muhimmiyar hanya ce za a bi domin daidaita hargitsin Somali?

cri

Cikin wani lokaci na kusa-kusa da ya wuce, an yi hargitsin makamai mafi tsanani wanda ba a taba ganin irinsa ba tun rabin shekara da ya wuce a kasar Somali. Ban da dakarun rukunonin addinai da gwamnatin wucin gadi wadanda suka shiga cikin wannan hargitsi, kuma kungiyoyin dakaru na kasashen waje su ma sun sa hannu cikin hargitsin, shi ya sa halin da ake ciki wajen hargitsin ya kara yamutsewa. Manazarta sun nuna damuwa cewa, idan da ba a shawo kan hargitsi ba, mai yiwuwa ne duk shiyyar da ake kira kuryar Afirka za ta shiga cikin wani yaki. Sabo da haka, cikin 'yan kwanakin nan da suka wuce, kwamitin sulhu na M.D.D. da kawancen Afirka da kawancen kasashen Larabawa sun yi taron gaggawa kan matsalar Somali, inda suka kirayi sassa daban-daban da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta nan da nan, kuma su sake yin shawarwari. Sun bayyana cewa, sake yin shawarwari da kuma daddale yarjejeniyar siyasa tsakanin gwamnatin rikon kwarya da dakarun rukunonin addinai sun zama muhimmiyar hanya ce za a bi domin daidaita matsalar.

Tun shekarar 1991 zuwa yanzu, kasar Somali kullum tana cikin halin fama da makamai. A shekarar 2004, bisa goyon bayan da ta samu daga kasashen duniya, Somali ta kafa gwamnatin rikon kwarya. Amma sabo da rashin karfi, gwamnatin rikon kwarya kullum ba ta iya tafiyar da mulkinta mai amfani ga duk kasa ba, sa'an nan kuma shawarwarin da ake yi tsakaninta da dakarun rukunonin addinai domin shimfida zaman lafiya shi ma ya samu ci gaba kadan-kadan.


1  2  3