Manazarta sun bayyana cewa, hargitsin Somali ya kasu kashi 2, a bayyane sabani ne da ake yi tsakanin kawancen kotunan Islama na kungiyar dakarun rukunonin addinai da gwamnatin rikon kwarya, a hakika kuwa gwaje-gwajen karfi ne da ake yi tsakanin kasashen 2 wato Habasha da Eritrea. A shekarar 1998, Habasha da Eritarea sun taba gwabzawa da juna sabo da hargitsin iyakar kasa a tsakaninsu, ko da yake bangarorin sun daddale yarjejeniyar zaman lafiya a karshen shekarar 2000 bisa aikin sulhu da sassa daban-daban suka yi, amma bangarorin 2 sun yi ta yin ja-in-ja a lokacin da suke gudanar da yarjejeniyar, shi ya sa da kyar aka samu ci gaba wajen bincike domin tabbatar da iyakar kasa a tsakanin Habasha da Eritrea. Sabo da wadannan kasashe 2 dukkansu ba su fatan ganin wani mulkin Somali wanda ba shi da amfani ga kasashensu na kansu, shi ya sa sun yi kokarin yin shisshigi cikin hargitsin Somali.
1 2 3
|