Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 16:41:16    
Yawan sojojin Amurka da suka mutu a cikin yakin Iraki ya kai fiye da yawan mutanen da suka mutu a cikin al'amarin "9.11"

cri

Bisa wani rahoton bincike daban da aka yi, yanzu yakin Iraki yana shafar Amurkawa. Yawancinsu suna ganin cewa bai kamata Amurka ta yi watsi da yakin Iraki ba, amma a sa'I daya kuma suna tsamani hasarar yaki ta yi yawa; suna fatan sojoin Amurka su janye jiki daga Iraki, amma suna nuna damuwa cewa Iraki za ta shiga rikici bayan haka; suna goyon baya shawarar da "kungiyar nazarin batun kasar Iraki" ta yi, amma ba su san abubuwan da ke cikin shawarwarin ba, shi ya sa, ba su san ko ya kamata gwamnatin Bush ta karbi wannan shawarwari. Yawan sojojin Amurka da suka mutu ya kai fiye da yawan mutanen da suka rasu a cikin karmakin "9.11" zai sa su shiga uku kuma za su kara damuwa.

A sa'i daya kuma, karuwar yawan mutuwa ta karya zakatan sojojin Amurka da ke kasar Iraki. Bisa gwajin da aka yi ga sojojin Amurka da ke Iraki kan a fannin karfin zuciya, an ce, akwai kashi 13.6 cikin kashi 100 da suka kamu da irin ciwon hankali. kuma al'amuran kisan kai sun faru da yawa.

A wata mai zuwa, gwamnatin Bush za ta fitar da sabbin manufofi kan Iraki. Amma, wasu kwararru sun yi bakin ciki da nuna cewa, zabe maras kyau ne gwamnatin Amurka ta yi game da manufofin da take aiwatarwa kan kasar Iraki. Don haka, babau wata kyakyawar makoma ta kyautata halin da ake ciki a kasar Iraki.(Musa)


1  2  3