Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 16:41:16    
Yawan sojojin Amurka da suka mutu a cikin yakin Iraki ya kai fiye da yawan mutanen da suka mutu a cikin al'amarin "9.11"

cri

Ran 26 ga wata, bangaren sojojin kasar Amurka ya ba da labari cewa, akwai sojojinsa shida da suka mutu a kasar Iraki. Wannan ya sa jimlar yawan sojojin Amurka da suka mutu a cikin yakin Iraki ya kai 2977 tun lokacin da aka fara yin yakin Iraki a shekarar 2003, wannan ya fi jimlar mutanen da suka mutu a cikin farmakin "9.11" da aka yi a shearar 2001 yawa da mutane hudu. An bayar da wannan labari a lokacin hutu na Christmas, wannan ya kawo bakin ciki yayin da ake yi bikin Christmas. Wasu manazarta sun yi hasashen cewa, ana ta samun tashe-tashen hankula a kasar Iraki, kuma sojojin kasar Amurka da ke mutuwa a kasar suna ta karuwa, duk wadannan sun kawo cikas ga gwamnatin Bush, da sojojin kasar da kuma jama'ar kasar.

A watan Maris na shekarar 2003, gwamnatin Bush ta yi biris da kiyewar da kasashen duniya suka yi mata, ta kyale kwamitin sulhu na MDD har ta kafa "Kungiyar taron dangi" don afka wa kasar Iraki da yaki don hamburar da mulkin Saddam Hussein.

Amma, bayan sojojin Amurka sun yi binciken duk kasar Iraki, ba su sami dalilin tayar da yakin Iraki na cewar wai ya kasance da "makamai masu kare dangi" a kasar ba. Wani dalilin daban da ya sa gwamnatin Bush ta kai farmakin yaki a Iraki shi ne zagin dangantaka tsakanin gwmnatin Saddam Hussein da kungiyar "al-Qaida" wadda ta kai harin "9.11" tana da kyau. Amma, har yanzu, ba ta sami wata shaida ba don tabbatar da wannan dalili. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne 'yan jam'iyyar dimokuradiyya masu adawa su zargi wannan da babbar murya. Sun ce, babu wata shaida da za ta iya hada yakin Iraki da harin "9.11" da 'yan ta'ada suka yi. kuma yakin Iraki ya rage karfin Amurka wajen yaki da ta'adanci, har yanzu ba a kama Bin Laden jagoran kungiyar "al-Qaida" ba, kuma kasar Afghnistan tana cikin halin tsaka mai wuya.


1  2  3