Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-27 16:41:16    
Yawan sojojin Amurka da suka mutu a cikin yakin Iraki ya kai fiye da yawan mutanen da suka mutu a cikin al'amarin "9.11"

cri

Ko da ya ke kullum gwamnatin Bush tana jaddada cewa sojojin Amurka za su ci nasarar yakin Iraki, amma, saboda karuwar al'amuran tashin hankali da kisan gillar da ke tsakanin marhabobi a kasar Iraki, shi ya sa shugaba Bush na kasar Amurka ya tsaida kudurin sallami Mr. Donald Rumsfeld ministan tsaron kasa na Amurka wanda ya jagoranci yakin Iraki.

Daga baya, a farkon watan nan, "kungiyar nazarin batun kasar Iraki" ta bayar da wani rahoto cewa, halin da ake ciki a kasar Iraki "yana da tsanani sosai, kuma ya yi ta yin tsami". Mr. Robert Gates sabon ministan tsaron kasa na Amurka ya ce, kasar Amurka ba ta ci nasarar yakin Iraki ba. Fuskantar mawuyancin halin da ake ciki a kasar Iraki, a ran 18 ga wata, karo na farko shugaba Bush na kasar Amurka ya yarda da cewa kasar Amurka ba ta samu nasarar yakin Iraki ba. Yanzu gwamnatin kasar Amurka tana dauki babban nauyi, har kullum 'yan jarida na kasar Amurka sun tambaya shugaba Bush ko ya iya yi barci da dare!

Game da jama'ar kasar Amurka, su fara fahimta mene ne yakin Iraki ya kawo kasar Amurka sannu sannu. Bisa wani sakamakon kididdigar da aka bayar a ran 18 ga wata, yawan mutanen da suke goyon baya manufofin Iraki da kasar Amurka take tafiya ya kai mafi karanci na kashi 28 cikin kashi 100. a sa'i daya kuma, yawan mutane masu adawa ya kai mafi yawa na kashi 70 cikin kashi 100.


1  2  3