Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-25 16:00:32    
Rikicin da ake yi a kasar Somaliya ya kara tsanani

cri

Amma kasar Eratrea da ke da huldar gargajiya ta yin adawa da kasar Habasha ta nuna goyon bayanta ga dakarun rukunin addinai. Tun daga shekarar 1993, bayan da kasar Eratrea ta sami yancin kai daga kasar Habasha , sai kasashen biyu suna ta yin hargitsi a tsakaninsu. Daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2000, an tayar da babban hargitsin makamai a iyakar kasa da ke tsakanin kasashen biyu, kodayake bangarorin biyu sun daddale wata yarjejeniyar dakatar da yaki a tsakaninsu, kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su ma sun girke a iyakar kasashensu, amma ba a daidaita gardamar da ke tsakaninsu ba, yin adawa da juna a tsakaninsu bai taba tsayawa ba. A lokacin da kasar Habasha ta tura sojojinta don nuna goyon baya ga gwamnatin rikon kwarya, to tabbas ne kasar Eratrea ta tura sojojinta don nuna goyon baya ga kawancen kotuna na Islamia.

Mazaunan da ke zama a iyakar kasar Somaliya sun bayyana cewa, bisa kiran da kawancen kotuna na Islamic suka yi da cewar wai dukan jama'ar kasar su shiga cikin rundunar sojojin da ke yin adawa da sojojin Habasha, sai a kwanan baya, daruruwan musulmin kasashen waje suka shiga cikin kasar Somaliya. Yawan sojojin da kasar Habasha ta tura zuwa kasar Somaliya ya kai dubu 8, kuma yawan sojojin kasar Eratrea a kalla ya kai dubu 2. manazartan al'amarin nan sun bayyana cewa, mai yiyuwa ne za a haifar da rikicin da ke kara tsanani a shiyyar nan.(Halima)


1  2  3