Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-25 16:00:32    
Rikicin da ake yi a kasar Somaliya ya kara tsanani

cri

Tun daga shekarar 1991 har zuwa yanzu, kullum kasar somaliya tana kasancewa cikin halin rashin samun tsayayyar gwamnati wadda azzaluman yaki suke rarraba ikon mulkin kasar. A shekarar 2004, aka kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar Kenya, a shekarar 2005, gwamnatin ta koma gida kasar Somaliya, amma bisa sanadiyar rashin hakikanin karfi ne, ba ta iya sarrafa duk kasar ba. Ba sau daya ba ba sau biyu ba gwamnatin rikon kwarya ta kirayi gamayyar kasa da kasa da ta aika rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar somaliya don taimaka wa gwamnatin tsakiya wajen aiwatar da ikon kula da harkokin kasa, amma dakarun rukunin addinai sun nuna kiyayyarsu, sun ce, za a mayar da dukan sojojin kasashen waje da ke girke a kasar somaliya bisa matsayin sojoji masu kai hari.

A ranar 12 ga wannan wata, kawancen kotuna na Islamic ta kuma bayar da sanarwar karshe ga sojojin kasar Habasha da ke girke a kasar Somaliya cewa, dole ne su janye jikinsu daga kasar Somaliya a cikin mako guda. A ranar 19 ga wannan wata da dare, sa'o'I biyu ya wuce bayan da aka bayar da sanarwar karshe, dakarun rukunin addinai sun soma aikinsu, sun kai farmaki kan sansanoni biyu na horas da hafshoshin sojoji na kasar Habasha a wurin da ke dab da birnin Baidoa. Gwamnatin rikon kwarya da sojojin kasar Habasha nan da nan ne suka kai harin ramuwa . Daga nan rikicin da ke tsakaninsu sai kara tsanani yake yi.

Kasar Somaliya da kasar Habasha sun kasance cikin ja in ja kan yankunan kasa cikin dogon lokaci a tarihi, a wurin, ana kasancewa cikin yamutsatsen hali a fannin abubuwan tarihi da addinai. Amma kawancen kotunan Islamia yana son kafa wata babbar kasar Somaliya wadda ke kunshe da kasar Habasha da Kenya da Djioubti.


1  2  3